Back Home News Sama da janar-janar 100 za su yi ritaya a sojin Najeriya
gaskiya24.wapka.co

Sama da janar-janar 100 za su yi ritaya a sojin Najeriya


Kimanin manyan hafsoshin soja 100 da suka hada da janar-janar, na sojin kasa da na sama da kuma na ruwa na Najeriya za su yi ritayar dole sakamakon nadin sabbin hafsoshin tsaro da shugaban kasar Bola Ahmad Tinubu ya yi a baya-bayan nan.

Baya ga shirin ritayar da ake shirin yi, za a kara wa jami’ai da dama girma zuwa matsayi na gaba don cike guraben da manyan hafsoshin da za su yi ritayar.

Hakan dai na faruwa ne watanni shida bayan da wasu manyan hafsoshin soja 24 da birgediya-janar 38 suka yi ritaya a watan Disambar da ya gabata bayan shafe shekaru 35 suna aiki.

Dama dai al’ada ce a aikin soja, idan aka nada na kasa a matsayin shugaba na saman su ajiye aiki, don ana fargabar watakila ba za su iya karbar oda daga wajensa ba. TALLA

Ritayar dai za ta shafi `yan aji na 36 da 37 da kuma aji na 38, wadanda suka fara aiki tun kafin wadanda aka nada, da kuma wadanda suke mataki daya da su.

Me ya sa ake yi wa wasu sojoji ritaya kafin naɗa sabon babban hafsa? 28 Mayu 2021

Lokaci huɗu da rundunar sojin saman Najeriya ta shiga makoki 22 Fabrairu 2021 Nawa ne slashing 'yan sandan Najeriya?

15 Yuli 2020 Me masana ke cewa ? Wasu manyan sojojin Najeriya
Related post

Select Category

  • Select Category